Amurka
Yar wasan fina finan Amurka Taylor ta bar duniya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Elizabeth Taylor shahararriyar ‘yar wasan fina finai na kasar Amurka ta bar duniya tana da shekaru 79 da haihuwa.Ta gamu da ajalinta a birnin Los Angeles, tana cikin ‘yan wasan da suka yi suna cikin karni na 20.An haifi Elizabeth Taylor a shekarar 1932, kuma tana cikin wadanda tautaronsu ya yi tashe cikin harkar fina finai a duniya.