FARANSA

Faransa tace wata daya yayi yawa su karya Gaddafi

Ministan Harakokin wajen Faransa Allain  Juppe
Ministan Harakokin wajen Faransa Allain Juppe

Ministan hararokin wajen kasar Faransa Allain Juppe ya bayyana cewa kwanaki ne ko makwanni kawai zai dauki taron dangin kasashen yammaci wajen karya dakarun Muammar Gaddafi.Ministan ya bayyana cewa fatansu shi ne nema wa kasashen larabawa ‘yancinsu na neman sauyi a kasashensu. A cewarsa akwai nasara tare da kwarin gwiwa a yakin da suke yi da libyaMinistan yace matakin kasashen yammaci shi ne kare fararen hula daga hare haren da dakarun Gaddafi ke kaiwa, ministan kuma ya karyata rehotannin da ke cewa suna kasha fararen hula.