NATO/OTAN

NATO/OTAN ta dauki alhakin haramta shawagin jirage a Libya

wani jirgin tsaron NATO/OTAN
wani jirgin tsaron NATO/OTAN Reuters/Alessandro Garofalo

Kungiyar Tsaron arewacin tekun Atlantika ta NATO ko OTAN ta amince da karbar ragamar tafiyar da tsarin Majalisar Dunkin Duniya na haramta shawagin jiragen sama a sararin samaniyar kasar Libya bayan shiga kwanaki bakwai na taron dangin kasashen yammaci.Bayan tattauanawa na tsawon lokaci musamman da kasar Turkiya wadda ta nuna adawa, a karshe kungiyar ta amince da shiga gaba wajen aiwatar da kudirin na Majalisar Dunkin Duniya.Sakatare kungiyar Anders Fogh Rasmussen ya tabbatar da karbar wannan aiki inda ya bayyana cewa sun karbi wannan kudirin ne na kasashen turai domin kare rayukan fararen hula daga bala’in da suke a ciki na mulkin Gaddafi.Tuni dai Prime Ministan Birtaniya David Cameron ya yi maraba da wannan mataki na NATO a matsayin matakin ci gaba.