Guatemala

Uwargidan Guatemala ta nemi raba aurenta da shugaban kasa

Uwargidan Shugaban kasar Guatamala Sanda Terres da Mijinta shugaban kasa
Uwargidan Shugaban kasar Guatamala Sanda Terres da Mijinta shugaban kasa REUTERS/Khaled al-Hariri

Matar shugaban kasar Guatemala Sandra Torres de Colom ta bayyana shirin raba aurenta da shugaban kasar, domin saman damar takarar shugabancin kasar a watan Satumba mai zuwa.Ta bayyana cewa zata rabu da mijinta domin auren al’umar kasar da take neman kuri’unsu a zaben kasar na watan Satumba.Tsarin mulkin kasar ta Guatemala ya haramta wa masu dangantaka da shugaban kasa tsayawa zabe, kuma tuni masu nazarin harkokin siyasar kasar suka fara sukar haka cewa yaudara ce da wayo, amma shugaba Alvaro Colom ya musanta zargin.