Canada

Gwamnatin kasar Canada ta PM Harper rushe

PM Canada Stephen Harper, a majalisar dokokin kasar
PM Canada Stephen Harper, a majalisar dokokin kasar REUTERS/Chris Wattie

Gwamnatin PM Stephen Harper ta kasar Canada ta rushe, bayan kuri’ar yanke kauna da aka kada mata a majalisar dokokin kasar.Jam’iyyar adawa ta Liberal Party ta janyo kada kuri’ar ta yanke kauna da taimakon wasu kananan jam’iyyu, kuma haka ya tilasta gudanar da zabe farkon watan Mayu mai zuwa.Yau Asabar ake saran PM kasar ta Canada Harper, zai neman Shugaban kasar David Johnston ya rusa majalisar dokoki, sannan za a kashe kwanaki 36 ana yakin neman zabe.