Yemen

Shugaban Yemen Saleh ya shirya sauka daga mulki

Reuters / Stringer

Shugaban kasar Yemen Ali Abdullah Saleh, ya bayyana cewa a shirye ya ke ya yi ban kwana da madafun ikon kasar, wanda haka zai mayar da shi shugaban kasar Larabawa na uku da boyen al’uma ya sallama daga bakin aiki.Saleh ya kara da cewa zai ajiye aiki ne kawai, inda zai mika da hanun da ya dace, kamar yadda ya shaida wa taron magoya bayan sa. Wasu majiyoyin sun bayyana cewa ana tattaunawa ta bayan fage, wadda Shugaban kasar ta Yemen zai sauka cikin tsanaki da kwanciyar hankali.Jiya Jumma’a dubban mutane sun fito gangamin neman Shugaba Abdullah Saleh ya yi murabus, a Sana’a babban birnin kasar.