Siriya

Zanga zangar adawa da gwamnatin Siriya ta fadada

REUTERS/Nada Fares

An gudanar da gagarumin zanga zanga cikin biranen kasar Siriya da suka hada da Damascus babban birnin kasar, domin nuna adawa da gwamnati, kwana daya bayan gwamnati ta bayyana shirin kwarya kwaryar sauye sauye.Akalla mutane 10 sun hallaka, masu raji kare hakkin bil Adam sun zargi dakarun gwamnati da bude wuta. Inda ake cewa kimanin mutane 55 sun hallaka cikin mako guda da aka kwashe ana zanga zanga, wa gwamnatin Bashar al-Assad.Anji karar bindigori a garin Deraa na kudancin kasar ta Siriya, inda shugaba al-Assad ke fuskantan kalubale mafi tsauri a tsawon mulkinsa.Magoya bayan shugaban sun yi nasu zanga zangar ta goyon baya, wadda ta janyo kai ruwa rana da masu adawa a Damascus babban birnin kasar.