Siriya

Mutane shida sun hallaka nasadiyar rikicin siyasar Siriya

Reuters/Stringer

Akalla mutane shida sun hallaka cikin kwanaki biyu da aka yi ana zanga zangar nuna kiyayya wa gwamnatin kasar Siriya, a garin Latakia mai tashar jiragen ruwa.Masu raji kare hakkin bil Adam sun zargi dakarun kasar da bude wuta kan masu zanga zangar, inda aka samu mutuwan mutane masu yawa, tun fara macin neman gudanar da sauye sauye demokaradiya.Shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad, yana fuskantar kalubale mafi tsauri a tsawon mulkinsa na shekaru 11, yayin da zanga zangar adawa ke rurutuwa kamar wutar daji.