Canada

Ranar Biyu ga watan Mayu zaben kasar Canada

PM kasar Canada Stephen Harper, ya bayyana ranar biyu ga watan Mayu, a matsayin ranar da za a gudanar da zaben kasa baki daya.PM ya bayyana haka a Ottawa babban birnin kasar, bayan ganawa da Shugaban kasar David Johnston, wakilin Sarauniyar Ingila Elizabeth na II, wanda ya rusa majalisar dokoki, kamar yadda tsarin mulkin kasar ya tanada.Ranar Jumma’a data gabata, gwamnatin kasar at Canada karkashin PM Harper ta rushe, kuma yanzu an bude yakin neman zabe ke nan. 

PM Canada Stephen Harper
PM Canada Stephen Harper REUTERS/Chris Wattie