Birtaniya

Zanga zangar kan rage kashe Kudaden Gwamnati a Birtaniya

REUTERS/Paul Hackett

Dubban mutane sun halarci macin nuna adawa da shirin gwamnatin kasar Birtaniya na zabtare kudaden da gwamnati ke kashewa, domin jin dadin jama’a.Macin wanda aka gudanar a tsakiyar birnin London, ya samu halartar shugaban jam’iyyar adawa ta Labour Ed Miliband, wanda ya gudanar da jawabi wa masu zanga zangar.Ministocin gwamnatin kasar ta Birtaniya sun kare matakin da cewa zai taimaka wajen daidaita tattalin arzikin kasar.