Siriya

Ana ci gaba mayar da martani bisa jawabin shugaban Siriya

Shugaban Siriya Bashar el-Assad
Shugaban Siriya Bashar el-Assad Reuters/Syrian state TV

Kasashen Yammacin Duniya da kuma 'yan adawar kasar Siriya, na ci gaba da bayyana bakin cikinsu kan jawabin shugaba Bashar al Assad, dangane da sauye sauye a kasa.Mutane da dama sun yi hasashen shugaban zai soke dokar ta baci da aka kafa a kasar, wanda masu zanga zanga suka bukata, amma hakan bai yiwu ba.Shugaban ya amince da cewa akwai bukatar kawo sauye sauye, amma babu wata hanyar kawowa da ya bayyana yayin jawabin wa al'umar kasar.