Cannes Festival

Mata zasu haska a gasar Fina-Finai ta Cannes

Julia Leigh (G), ta Fim din «Sleeping Beauty» tare da Emily Browning, a Gasar Cannes
Julia Leigh (G), ta Fim din «Sleeping Beauty» tare da Emily Browning, a Gasar Cannes REUTERS/Yves Herman

‘Yan Fim Mata daga sassan kasashen Duniya ne zasu halarci gasar Fina Finai ta Cannes karo na 64 da za’a kwashe mako daya ana gudanarwa daga 11 ga watan Mayu zuwa 22 na wannan Shekarar.A bukin dai za’a fitar da zakara a fagen Fim na wannan shekarar ta 2011. Kuma ‘yan Fim ne daga kowane sako zasu halarci gagarumin bukin wanda za’a gudanar a birnin Cannes.Akwai dai Fina Finai sama da Ashirin da aka shigar masu neman lashe kyautar Fim din da yafi shahara a shekarar 2011. daya daga cikinsu shi ne Fim din ‘Hanezu’ na wani dan kasar Japan Naomi Kawase wanda ke magana kan al’adun kasar Japan.