Amurka

Dominique Strauss Khan zai gurfana a gaban kotu

Dominique Strauss-Kahnhitowar shi daga ma'aikatar yan sanda ta garin  Harlem
Dominique Strauss-Kahnhitowar shi daga ma'aikatar yan sanda ta garin Harlem REUTERS/Allison Joyce

A yau litanin ne, ake sa ran gurfanar da shugaban FMI - assusun bada lamani na duniya, dan kasar Fransar nan Dominique Strauss kahn,a gaban kotu . Tun jiya dai ‘yan sandar birnin New York na kasar Amruka ke tsare da shi, sakamakon zargin yunkurin aikata masha’a da wata ma’aikaciyar Hotel, al’amarin da ke yinkurin wargaza mafalkinsa na neman kujerar shugabancin kasar Fransa a 2012.