MEXICO

An Gano Bakin Haure fiye da 500 a manyan motoci a Mexico

© REUTERS/Striger

Rundunar 'yan sanda kasar Mexico ta yi nasarar gano bakin haure 513 makale a cikin wasu manyan motocin dakon kaya guda 2 a Chiapas, jihar dake yankin kan iyakar kudu maso gabashin kasar ta Mexico, kamar yadda babban lauyan yankin ya sanar.Kakakin ma’aikatar ministan dake kula da al’ummar kasar ya bayyana cewa, wannan shine ceton bakin hauren da ke tafiya cikin mawuyacin hali da aka taba yi a kasar ta Mexico.