Amurka-Birtaniya
Kasashen Amurka da Birtaniya sun jaddada hadin kan dake tsakani
Wallafawa ranar:
Shugaban Amurka Barack Obama ya shaida wa PM Birtaniya David Cameron cea dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta musamman ce.Yayin taron manema labarai a birnin London na kasar Birtaniya, shugabannin biyu sun jaddada matsayin ganin shugaban Libya Muammar Gaddafi ya yi ban kwana da madafun iko, bayan mulkin shekaru 42.Tunda fari PM Birtaniya Cameron da shugaban Amurka Obama sun gana a fadar mulkin kasar ta Birtaniya, game da abunda ke faruwa a kasashen Afghanistan da Libya.