G8

G8 sun goyi bayan Obama kan rikicin Isra’ila da Palasdinawa

Shuwagabannin kasashe masu karfin tattalin arziki na G8 sun goyi bayan bukatun shugaban Amurka Barrack Obama kan Isra’ila ta amince da yarjejeniyar iyakokinta da Palasdinawa na shekarar 1967. Sanarwa data fito daga dakin taron kasashen na G8 a Deauville can arewacin Faransa, shugabannin sun bukaci gwamnatin Isra’ila da Palasdinu da su yi kokarin komawa a teburin tattaunawa domin kawo karshen takaddamar dake tsakaninsu.A lokacin da shugaba Obama ke ganawa da Benjamin Nethanyahu a Woshington, Mista Obama ya yi kira ga Isra’ila da Palasdinawa da su amince da yarjejeniyar iyakokinsu ta shekara 1967 a matsayin matashiya domin kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu.Sai dai kuma Prime Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da bukatun na Obama.  

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy  da  Barack Obama na Amurka a Taron G8 à Deauville.
Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy da Barack Obama na Amurka a Taron G8 à Deauville. Reuters/Jewel Samad