G8

Taron kasashe masu karfin tattalin arziki na G8

Shugaban Amurka Barrack Obama da takwaransa na Faransa Nicolas Sarkozy a taron G8 a  Deauville can arewacin Faransa
Shugaban Amurka Barrack Obama da takwaransa na Faransa Nicolas Sarkozy a taron G8 a Deauville can arewacin Faransa

A taron da ake gudanarwa na kasashe 8 masu karfin tattalin arzikin duniya a kasar Faransa, a yau Juma’a shuwagabannin kasashen zasu cim ma hanyar da zasu taimakawa kasashen larabawa masu fama da zanga-zangar neman tabbatar da Demokradiyya tare da daukar matakin ganin Muammar Gaddafi ya yi ban kwana da madafan ikon kasar Libya.Kasashen na G8 da suka hada da Birtaniya da Faransa da Amurka da Italiya da Canada da Japan da Rasha da Jamus sun yi kira ga gwamnatin kasar Siriya da ta gaggauta kawo karshen amfani da karfi wanjen murkushe masu gudanar da zanga-zanga.Taron ya samu halartar shuwagabannin kasashen Tunisia da Masar da wakilan Majalisar Dunkin Duniya tare da wakilan kungiyar kasashen larabawa.Prime Ministan Birtaniya David Cameron a jiya Alhamis ya yi alkawalin tallafawa kasashen da kudin Euro Militan 110 domin tabbatar da demokradiyya a kasashen na larabawa. Haka kuma ana sa ran shugaban kasar Faransa Sarkozy zai bayyana tallafinsa.Kazalika, taron ya samu halartar wasu daga cikin sabbin shugabannin kasashen Africa da aka rantsar a kwanan nan da suka hada da shugaban Cote d’Ivoire da shugaban Jamhuriyyar Niger da kuma shugaban kasar Guinea.