FIFA

Rikicin hukumar kwallon kaffa ta duniya FIFA

Shugaban hukumar kwallonkaffa ta duniya Fifa,  Jospeh Blatter
Shugaban hukumar kwallonkaffa ta duniya Fifa, Jospeh Blatter REUTERS/Arnd Wiegmann

Yau ne ake saran gudanar da zaben shugaban Hukumar Kwallon kafa ta Duniya, mai fama da rikici, sakamakon zargin cin hanci da rashawa daya mamaye shugabanin Hukumar, kuma Joseph Blatter kadai ne ke takara shugabancin ta.Kasar Ingland, wanda tayi fushi saboda rashin samun damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya, na yunkurin ganin an dage zaben, amma Hukumar FIFA ta ce za ta ci gaba da zaben.Alh Ibrahim Galadima, Tsohon shugaban Hukumar kwallon kafa a Najeriya, ya yi tsokaci akai. Dangane da zargin cin hancin da akewa shugabanin Hukumar kwallon kaffa ta Duniya, daya daga cikin jami’an ta, Franz Baukenbauer, ya ce zargi ne kawai akewa jami’an, tun da har yanzu babu wata shaida.Ga kuma abun day a ke cewa:‘Wannan duk zargi ne, ina kiran sa zargi saboda babu wata shaida, babu shaida, kuma an fara samun haske, wanan hukuma ta Blatter, an haife shi da ita, saboda ya kwashe kusan shekaru 40 ya na cikin ta.’