Amurka

Fiye da Rabin Matasan Amurkawa na kwankwadar Barasa

Guillaume Calas

Wani Bincike da Cibiyar dake kula da lafiya da kuma hana anfani da miyagun kwayoyi na Amurka tayi, ya nuna cewar, sama da rabin Amurkawa da suka zarce shekaru 12, na kwankwadar barasa, yayin da kashi daya daga cikin hudu kuma, suka amsa cewar sun busa tabar wiwi.Binciken da Cibiyar ta gudanar ya nuna cewar, Amurkawa dake tsakanin shekaru 18 zuwa 25, a Jihar New Hampshire ne, suka fi shan barasar.