Amurka

Kare ya bada shaida a wata kotun Amurka

Karen da ya bada Shaida a kotu
Karen da ya bada Shaida a kotu Rfi

A karon Farko, hukumomin birnin New York, dake kasar Amurka, sun baiwa wani kare damar bada shaida a kotu, kan shari’ar fyade da wata yarinya mai shekaru 15 ke yiwa mahaifinta, abinda ya kai ga yi mata ciki.Rahotanni sun ce, alkalin kotun ya baiwa Karen mai suna Rosie, damar shiga inda ake bada shaida, tare da yarinyar, lokacin da ake ta sauraron karar.Mahaifin yarinyar ya daukaka kara, kuma ana saran yarinyar da karenta zasu sake komawa kotu, dan bada shaida.