Tattalin Arzikin Duniya

Kasuwannin duniya na cikin Fargaba

Kasuwar Hannayen Jarin yankin ASiya
Kasuwar Hannayen Jarin yankin ASiya Reuters

Kokarin da shugaban Amurka Barrack Obama ke yi da sauran manyan kasashen duniya wajen kokarin farfado da darajar tattalin arzikin duniya ya saka kasuwannin duniya cikin fargaba da shakku, yayin da kasuwannin hannayen jari ke ci gaba da faduwa.A safiyar yau Talata hannayen jarin kasashen Turai sun fadi kasa warwas al’marin da ke cusa shakku ga farfadowar kasuwar hannayen jarin.Manyan hannayen jarin duniya sai faduwa suke yi, inda Hannayen jarin Ingila suka fadi da kashi 4, na Frankfurt kuma da kashi 6, hannayen jarin Paris kuma sun fadi da sama da kashi 3.Masu saka hannayen jari, a yanzu haka sun zura ido ga sakamakon taron tattaunawa da babban bankin Amurka zai gudanar da zummar fitowa da wata sabuwar dabarar maganace matsalar.