Amurka

Akwai yiyuwar samun sauyi a Amurka

Shugaban kasar Amurka Barrack Obama.
Shugaban kasar Amurka Barrack Obama. REUTERS/Jason Reed

Wani Binciken jin ra’ayin jama’a da aka gudanar a kasar Amurka, ya nuna cewa, Amurkawa na fushi da ‘Yan Majalisun kasar, abunda ke nuna cewar, yawancinsu ba zasu samu komawa Majalisar ba, a zaben da za’ayi shekara mai zuwa.Binciken ya nuna cewar, kashi 24 na wadanda aka tuntuba ne suke goyan bayan sake zaben Yan Majalisun, saboda ganin yadda aka samu matsalar tattalin arziki.Shi kansa shugaban kasa, Barack Obama bai tsira ba, ganin kashi 51 na Amurkawa, basa goyan bayan sake zaben sa.Sai dai ya zuwa yanzu, babu wani Dan takara da ake ganin zai iya kalubalanatar sa, duk da cewa, farin jininsa ya ragu, inda yake da kashi 49.