Tattalin Arzikin Duniya

Hannayen jarin Asiya sun fara farfadowa

wani Dan kasuwa yana hasashen yadda kasuwar hannayen jari ta kaya.
wani Dan kasuwa yana hasashen yadda kasuwar hannayen jari ta kaya. REUTERS/Paul Hanna

Hannayen Jari a kasuwannin kasashen Asiya sun fara farfadowa a yau laraba, sakamakon sanarwar da Bai-tulmalin Amurka ta bayar, na barin kudin ruwa yadda ya ke, a shekaru biyu nan gaba.Hannyen jarin Tokyo ya tashi da sama da kashi daya, na Sydney ya tashi da kusan kashi uku, yayin da na Seoul ya tashi da kusan kashi guda.Hannayen jari Hong Kong ya kai kusan kashi uku da rabi, Shangai kuma kuma kashi biyu, kamar yadda na Mumbai ya ke.