Tattalin Arzikin Duniya

Hannayen jarin kasawannin duniya sun fara farfadowa

wani Dan kasuwa yana hasashen yadda kasuwar hannayen jari ta kaya.
wani Dan kasuwa yana hasashen yadda kasuwar hannayen jari ta kaya. REUTERS/Lucas Jackson

Kasuwannin hannayen jarin kasashen duniya sun tashi a safiyar yau Juma’a bayan kwashe mako daya kasuwannin na fama da matsala. Kamar yadda Farashen danyen Man fetir ya tsaya cak akan kudi $85 duk ganga, Dala kuma tasha kashi akan Yen da Euro.A safiyar yau dai kasuwannin kasashen Turai sun tashi, inda hannayen jarin FTSE na Birtaniya suka tashi da kashi 0.3 akan kudi 5,178 hannayen jarin DAX na kasar Jamus kuma suka tashi da kashi 0.6 akan kudi 5,835, hannayen jarin CAC na kasar Paris kuma suka tashi da 0.1 akan kudi 3,092.Sai dai kuma hannayen jarin kasashen yankin Asiya na kokarin su daidaita bayan fama da matsala na ‘yan kwanaki.