Faransa-Jamus

Shagabannin Faransa da Jamus za su tattauna kan lamuran tattalin arzikin su

Shgaban faransa Nicolas Sarkozy tare da Waziyar Jamus Angela Merkel
Shgaban faransa Nicolas Sarkozy tare da Waziyar Jamus Angela Merkel Reuters

A yayin da kasuwanni hannayen jari na duniya suka dan farfado a jiya, a yau talata shugaban kasar Fransa Nicolas Sarkozy da waziriyar Jamus Angela Merkel, za su gudanar da zaman taron kan matsalar tattalin arziki a yankin kudin Euro na nahiyar Turai. A yau a birnin Pari shugaba Sarkozy zai tattauna da takwararsa ta Jamus Angela Merkel, manufar zaman taron dai da kasar jamus ta bukata shine, domin ganin kasashen biyu sun cimma dadaito kan yarjejeniyar da shugabannin kasashen turai yankin Euro suka cimma a ranar 21 ga watan da ya gabata, inda su kuma kasashen Farasar da Jamus zasu nazarta fannoni daban daban da ke kunshe a cikin yarjejeniyarHar ila yau Waziriyar Jamus da shugaban kasar ta Fransa, zasu tattauna bukatar samo hanyoyi mafiya inganci na magance matsalar tattalin arziki a yankin na Euro, kasashen turai dai na ci gaba da zaman zullumi dangane da matsalar tattalin arzikin da ta shafi wasunsu , musaman kasar Girka inda lamarin ya fi yin kamari.Yanzu haka dai kasuwannin hada hadar hannayen jari na turai sun fara farfadowa, inda a jiya suka rufe kofofinsu da riba, a yayinda shugaba Sarkozy ke neman wasu sababbin hanyoyin samun Karin kudin shiga a farnsa.