Amurka

Ana bincikar wata mace kan sakaci da danta a Amurka

Yara, baiwa daga Ubangiji
Yara, baiwa daga Ubangiji

A kasar Amurka yan sandan Massachusetts sun fara bincike kan wata ‘yar kasar Sweden data bar danta kan keken tura yara, taje sayen abinci.Yaron dan shekara guda, ya yi kimanin mintoci 10, kan keken yaran yayin da mahaifiyar ta shiga shagon sayan abinci, wannan ya jawo hankalin jami’an tsaro, saboda sakaci rashin kula.Amma matar ta shaida wa ‘yan sandan Amurka cewa haka ba laifi bane a kasar Sweden, sun saba barin yara a kafar shagon sayar da abinci.