FARANSA

Watakila yau a yi watsi da shara'ar Domic Straus-Khan

DSK da Nafisatou Diallo da ta zarge shi da Fyade
DSK da Nafisatou Diallo da ta zarge shi da Fyade REUTERS/Todd Heisler/Pool (L) and Shannon Stapleton (R)

NAN da Yan lokaci kadan ne ake saran kotu zata wanke Tsohon shugaban Hukumar Bada lamini ta Duniya, Domnique Strauss Kahn, daga zargin da ake masa na yunkurin fyade.Wanke Dominique Strauss Kahn zai bude wani sabon babi, a siyasar kasar Faransa, ganin cewar kafin tuhumar da aka masa, shine ake ganin zai iya raba shugaba Nicolas Sarkozy da karagar mulki.An dai zargi Tsohon shugaban Bankin ne da yunkurin fyade ga Nafisatu Diallo, a Manhattan, dake kasar Amurka, a ranar 14 ga watan Mayu, abinda ya kaiga gurfanar da shi a gaban kotu.Bincike da masana suka gudanar na jini, ya nuna cewar, kwayoyin halittar da aka samu a jikin rigar Nafisatou, sun yi dai dai da na Strauss Kahn, abinda ya sanya masu gabatar da kara gurfanar da shi a gaban kotu, da kuma tuhumar sa.Sai dai shari’ar ta samu nakasu, lokacin da aka fara tuhumar matar da take zargin, saboda abinda aka kira harshen damon da take yi kan lamarin, inda a karshe ake cewa, shaidun da ake da shi, ya nuna cewar bada yardar ta akayi ba.Kubucewa daga wannan shari’a, ba ta zama kare tuhumar da akewa Strauss Kahn ba, domin ko a kasar Faransa, akwai wata marubuciya da ta shigar da irin wanna kara.