UN-NIGERIA

Shugabannin duniya sun ci gaba da Allah wadai da harin bom a Nigeria

Harin ginin Majalisar Dunkin Duniya da aka kai a Abuja
Harin ginin Majalisar Dunkin Duniya da aka kai a Abuja AFP PHOTO/HENRY CHUKWUENDO

Shugannnin kasashen duniya sun ci gaba da yin Allah wadai da tashin bom din kunar bakin waken da aka yi a Nigeria, PM Britaniya David Camoron ya bayyana cewa lamarin abin takaici ne.Mr Cameron ya bayyana haka ne ne bayan tattaunawa da Sakatare Janar na MDD, Ban ki Moon, inda yace Nigria da kasar shi na fuskantar kalu bale iri daya, ya kuma yi tayin bayar da tallafi don zakulo wadanda suka yi aika aikar.