Australiya

Birnin Melbourne ya fi ko ina dadin zama a duniya

Wani binciken da masana suka yi, ya nuna cewa birnin Melbourne na kasar Ausralia ne ya fi kowanne dadin zama a duniya. Birnin na Melbourne ya yi wa birnin Vancouvan kasar Canada, daya yi shekaru a wannan matsayin fintinkau, inda yanzu Vancouvan ke matsayi na 3 bayan Vienan Austria.Binciken da aka yi kan birane 140, ya dora birnin Paris na kasar Faransa a matsayi na 16 yayin da kuma birnin London ke a matsayi na 53.Birnin da ya fi kowane rashin da a zama cikin wadabda a yi nazari shine Hararen kasar Zimbabwe.