Syria

A sanya takukumi kan Ministan harkokin wajen Syria

Ministan harkokin wajen Syria Walid Mouallem
Ministan harkokin wajen Syria Walid Mouallem REUTERS/Handout

A kokarin tan a dakatar da amfani da karfi da hukumomin kasar Syria ke yi kan masu zanga zanga, kasar Amurka ta sanya takunkumi kan ministan harkokin wajen kasar da wasu manyan jami’an Gwamnatin kasar 2. Wannan na nufin Walid Muallem da sauran mutane 2 ba za su yi wata hada hadar kasuwanci da kasashen waje ba.Wannan ne karo na 3 da hukumomin na Amurka ke daukar irin wannan matakin kan shugaba Bashar Al Asad da wasu jami’an gwamantin shi.