Amurka

Bukin tuna harin watan Satumba a Amurka

Shugaban kasar Amurka Barrak Obama tare da tsohon shugaba Geoge W Bush ne suka halarci tawayen ginin cibiyar hada hadar kasuwanci a bukin tuna shekaru 10 da kai wa cibiyar hari a 11 ga watan Satumba.Bukin ya hada da iyalan wadanda harin ya rutsa da su tare da shugaban gundummar birnin New York Michael Bloomberg da wanda ya gada Rudolph Giuliani wanda ya shugabancin gundummar shekaru 10 da suka gabata.Kimanin mutane 2,977 ne suka rasa rayukansu sanadiyar harin na watan Satumba, kuma Duk shekara ne kasar Amurka ke gudanar da bukin juyayin mutuwar wadanda suka mutu.Bukin wanda aka gudanar a ranar Lahadi ya samu tsauraran matakan tsaro a sassan yankunan birnin New York bisa wani gargadi da Amurka ta samu na kokarin kai mata hari. 

Shugaban Kasar Amurka Barack Obama tare da G. Bush da uwar gidansu
Shugaban Kasar Amurka Barack Obama tare da G. Bush da uwar gidansu