Amurka

An bayyana yakin Amurka a Iraqi a matsayin hasara

Tsohon kwamandan dakarun Amurka David Petraeus, a Kaboul.
Tsohon kwamandan dakarun Amurka David Petraeus, a Kaboul. REUTERS/Ahmad Masood

Bayan shekaru goma da Amurka ta kaddamar da yaki a kasashen Iraqi da Afghanistan, Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa kashi uku na dakarun Amurka da suka yi wa kasar aiki bayan kai harin watan Satumba sun bayyana yakin kasashen a matsayin babbar hasara ga gwamnatin kasar. Rahoton wanda ke bayyana sarkakiyar da Gwamnatin shugaba Barack Obama ke fuskanta, ya bayyana cewa, bayan shekaru 10 ana tafka yake-yake, lokaci ya yi da Amurka zata dai na zama uwa a siyasar duniya, don fuskantar matsalolinta na cikin gida.Rahotan yace, sojin Amurka 4,500 suka rasa rayukansu a Iraqi, 1,700 a Afghanistan, yayin da kuma kasar ta kashe Dala Trillion daya wajen gudanar da yake yaken.Bayan hasarar da yakin ya haifar ga Amurka, ya kuma jefa matsala wajen dangantaka tsakanin sojojin da iyalansu.Yanzu haka sojojin Amurka 98,000 ke kasar ta Afghanistan, yayin da kashi 41 na sojin da suka yi yaki a kasar ke cewa, kutsa kai yakin Afghanistan baya da wani tasiri ga Amurka.