Apple

Tsohon Shugaban kamfanin Apple, Steve ya mutu

Tsohon Shugaban kamfanin hada computar Apple, Steve Jobs, wanda ke fama da cutar sankara, ya rasu yana da shekaru 56.Sanarwar da kamfanin Apple ya bayar, ya bayyana basira da fasahar marigayin a matsayin abinda ya bunkasa rayuwar mutanen duniya baki daya.Shugaban kasar Amurka, Barack Obama, shugaban kanfanin Microsoft, Bill Gates, da Magajin Garin Birnin New York, Michael Blooomberg, sun bayyana kaduwarsu da mutuwar, saboda rawar da ya taka, da kuma basirar da Allah ya bashi. 

Tsohon shugaban Apple Steve Jobs
Tsohon shugaban Apple Steve Jobs Reuters