Venezuela

An ci tarar tashar talabijin a kasar Venezuela

Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez
Shugaban Kasar Venezuela Hugo Chavez Reuters路透社

Hukumar Dake kula da sadarwa a kasar Venezuela, ta ci tarar wata tashar talabijin Dala miliyan biyu, saboda rahotanni da ta bayar lokacin da aka yi zanga zanga a wani gidan yari na kasar.Daraktan hukumar, Pedro Maldonado, ya ce tashar wadda ta yi suna wajen sukar manufofin shugaban kasar ta Venezuela dake yankin Latin Amurka, Hugo Chavez, ta wuce gona da iri wajen rahotanni da ta bayar.