Myanmar
Ambaliyar Ruwa ta shafi tsakiyar Myanmar
Wallafawa ranar:
Mummunar ambaliyar ruwa ta shafi tsakiyar Myanmar inda mutane da dama suka salwanta da ke gabar Rafin Bank.Rahotannin daga kasar na cewa mutane 60 sun bace. Wani jami’in gwamnatin kasar ya shaidawa kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP, cewa ambaliyar tayi awon gaba da gidaje da ke bakin ruwa.Ya kara da cewa ruwan ya share wata gada da wani wuri da mabiya addinin kasar ke yin addu’a.