Argentina
Cristina Kirchner ta lashe zaben Argentina
Wallafawa ranar:
Shugaba Cristina Kirchner ce ta lashe zaben shugaban kasa karo na biyu da aka gudanar a kasar Argentina, bayan sakamakon farko sun nuna cewar ta samu sama da kashi 53 na kuri’un da aka kidaya, yayin da mai bi mata ya samu kashi 16.Tuni uku daga cikin ‘Yan takaran, cikinsu har da Tsohon shugaban kasa Eduardo Duhalde suka amince da shan kaye, kuma suka mika sakon taya murnar su ga shugabar.