Iran-Birtaniya-Jamus

An samu sabani tsakanin Birtaniya da Jamus kan Iran

Ministan harakokin Wajen Birtaniya William Hague
Ministan harakokin Wajen Birtaniya William Hague REUTERS/Ramzi Boudina

An samu rarrabuwar kai tsakanin kasashen Birtaniya da Jamus, kan daukar matakin soji akan kasar Iran, bisa zargin da ake mata na shirinta na makamin nukiliya.Wannan matsala ta fito fili ne yau, kafin fara taron Majalisar ministocin kungiyar kasashen Turai a Brussels, inda Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Haque, ya bayyana cewar, kasarsa ba ta fidda tsammanin amfani da karfin soji kan Iran ba a nan gaba.Sakataren yace, duk da yake ba yanzu ne suke shirin kaddamar da harin ba, amma basu kauda hakan ban an gaba.Shi kuwa takwaransa na Jamus, Guido Westerwelle, yace, kasarsa bata tunanin haka ko da wasa.Ministan yace, ba zasu shiga wani taro don tattauna amfani da karfin soji kan Iran ba, domin sun san cewa, irin wanna taro ba ya haifar da da mai ido.Ko a yau sai da shugaban Amurka, Barack Obama yace, zai tattauna da shugabanin China da Rusha, don daukar matsayi kan Iran.