Amurka

‘Yan sandan Amurka sun cafke mutumin da ya yi yunkurin halaka Obama

Oscar Ramiro Ortega-Hernandez, Mutumin da ya yi yunkurin kai wa Obama hari
Oscar Ramiro Ortega-Hernandez, Mutumin da ya yi yunkurin kai wa Obama hari REUTERS/United States Park Police/Handout

‘Yan Sandan kasar Amurka sun kama wani mutum mai shekaru 21, dan asalin kasar Spain, da ake zargin shi da yunkurin hallaka shugaba Barak Obama.Ma’aikatar shari’ar kasar tace ‘Yan sandan jihar Pennsylvania ne suka kama mutumin mai suna Oscar Ortega-Hernandez a ranar laraba, bayan da aka yi harbin da yunkurin kashe shugaban kasar a makon jiya.Obama da Uwargidansa Michelle dukkaninsu suna cikin Califonia lokacin da al’amarin ya faru Sai dai babu wanda ya sami rauni sakamakon harbin.Yanzu haka Ortega-Hernandez yana hannun ‘yan sandan bayan da alkalin kotu a yankin Pittsburgh, ya bada umurni, ana tunanin za’a yanke masa hukuncin daurin rai rai a gidan yari idan har aka tabbatar da zargin da ake ma shi.‘Yan sandan kasar sun cafke shi ne a wata Otel a Pennsylvania bayan an ji karar bindiga kusa da fadar White House.