Faransa-Jamus

Shugabannin Faransa, Jamus da Italiya sun fara wani taro

Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da Shugabar Gwmnatin Jamus Angela Merkel
Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy da Shugabar Gwmnatin Jamus Angela Merkel AFP / Jean-Christophe Verhaegen

Shugabannin kasashe 3 da suka firfin tattalin arziki a cikn masu amfani da kudin EURO sun fara wani taton a yau Alhamis, don tattauna wasu batutuwan da suka shafi kasashen yankin.Shuganban Faransa Nicolas Sarkozy ne zai karbi bakuncin shugabar gwamnatin Jamus Anjela Markel da sabon Prinme Ministan kasar Italiya Mario Monti da ya karbi madafun ikon kasar a makon da ya wuce, bayan da guguwar bashin da ta dabaibaye kasshen yankin, ta yi awon gaba da magabacin shi, Silvio Belisconi.Shugabannin za su duba yadda za a fidda kasashen yankin daga dimbin bashin da ya kai musu iya wuya.Za kuma su hada hannu wajen gaggauta cimma bukatar kasashen yankin 17, na kawo karshen rugurgujewar farashin hannayen jarin su.Yayin da ya rage watanni 5 kafin ya shiga zabe, shugaba Sarkozy na da wani Karin nauyin na daidaita darajar bashin kasar.Shi kuwa PM Italiya Monti, na fatan yin amfani da wannan ganawar, wajen dawo da karsashin kasar shi, a tsakani kasashen yankin.