Afghanistan-Jamus

Taron Afghanistan ya amince da ci gaba da tallafawa kasar

Taron makomar Afghanistan a kasar Jamus amma Pakistan ta kauracewa zaman Taron
Taron makomar Afghanistan a kasar Jamus amma Pakistan ta kauracewa zaman Taron Reuters

Taron kasashen Duniya Kan makomar kasar Afghanistan, ya amince da ci gaba da tallafawa kasar da  Taimako a shekaru goma nan gaba, muddin aka samu ci gaba wajen tafiyar da mulki a cikin kasar.

Talla

A jiya Litinin ne aka bude  taron kan makomar kasar Afghanistan, a birnin Bonn, na kasar Jamus, inda kasashen duniya suka halarci zaman taron, bayan gudanar da wani irinsa shekaru 10 da suka gabata.

A cewar Ban Ki-moon Sakatare Janar na Majalisar Dunkin Duniya, yanzu lokaci ne da za’a samu ci gaba don mika mulki, zuwa bunkasa harkokin rayuwa, wanda hakan ke nuna cewar, Afghanistan ta shiga wani lokaci na dangantaka da kasashen duniya, da kuma harkar tsaro ta duniya.

Sai dai a wannna karon, Pakistan ta kauracewa taron, saboda nuna bacin ranta kan yadda dakarun kungiyar NATO a karkashin Amurka suka kashe mata sojoji 24.

Sai dai kungiyar NATO ta nemi afuwar harin da ta kai ranar 26 ga watan Nuwamba wanda ya yi sanadiyar mutuwar dakarun Pakistan 24.

Da dadewa ne dai Amurka da kasashen Turai ke zargin kasar Pakistan da bada kariya ga kungiyar Taliban da kungiyar Haqqani da ake zargin kai hari a kan iyakar Afghanistan.

Kimanin wakilai 1,000 ne daga kasashen 100 suka halarci taron.

Sai dai masu sharhi sun kalubalanci matakin tsawaita zama cikin Afghanistan bayan kudirin kasashen Kawancen NATO na shirin ficewa daga Afhanistan a shekarar 2014.

Sakatariyar harakokin wajen Amurka Hillary Clinton tana daya daga cikin daruruwan wakilan kasashen da suka halarci taron.

Dakarun NATO sama da 500 ne aka kashe a bana cikin kasar Afghanistan.

An dade dai gwamnatin Afghanistan na neman hanyoyin sasantawa da kungiyar Taliban amma yunkurin ya gagara bayan kisan tsohon shugaban kasar Barhanuddin Rabbani wanda shugaba Karzai ya daurawa alhakin jagorancin sasantawar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI