Moody-EU

Kamfanin Moody zai yi nazari kan bashin Turai a badi

Wani dauke da wata tutar dake dauke da bayani akan kamfanin Moody
Wani dauke da wata tutar dake dauke da bayani akan kamfanin Moody Reuters

Kamfanin Moody da ke sa ido kan basukan kasashen duniya, ya ce zai yi nazari kan karfin basukan kasashen Turai 27, a farkon watanni uku a shekara mai zuwa.

Talla

Wannan mataki na Moody na zuwa ne a dai dai lokacin da takwaransa na ‘Standard and Poor’ ke cewa, yana nazarin rage darajar bashin kasashe 15 daga cikin 17 da ke amfani da kudin Euro, cikinsu har da manyan kasashe irin su Faransa da Jamus da ke mataki na uku.

Tuni dai kasuwannin hannayen jari suka fadi saboda gargadin kamfanin Moody.

Kamfanin na Moody yace, rashin matakin daidaita kasuwanni na karamin lokaci, ya nuna cewar, masu amfani da kudin Euro, da kasashen Turai, na fuskantar kalubale da kuma barazana kodayaushe.

An samu ci gaba a kasuwannin kasashen Asia yau Litinin, yayin da wasu masu zuba jari ke dari dari, saboda matakin da Birtaniya ta dauka a taron, yayin da Francois Hollande, dan takaran shugaban kasar Faransa, yace in ya lashe zaben, zai sauya matsayi kan matakin da Sarkozy ya dauka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI