Philippines

An kashe wani dan jarida a Philippines

Taswirar kasar Philippines
Taswirar kasar Philippines RFI/Anthony Terrade

An harbe wani dan jaridan kasar Philippine har lahira, yayin da aka yi kwanton bauna aka kai mishi harin, a kasar da ke daya daga cikin inda aka fi illata ‘yan jarida a duniya.Wani jami’in ‘yan sandan yankin Santos, da lamarin ya faru, yace wasu da ba a san ko su waye ba, sun zo kan babur, suka bude wuta ga Christopher Guarin yayin da ya ke cikin mota tare da iyalinshi da ‘Yarsa mai shekaru 9.

Talla

Harsashi ya sami mai dakin shi a hannu, amma kuma ‘Yar shi ta tsira ba tare da samun rauni ba. Kuma ‘yan sandan sun ce har yanzu ba wanda aka kama kan zargin hannu cikin kisan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI