Masar-IMF

IMF zata bada Tallafin kudi ga Masar

Shugabar hukumar Bada lamuni ta duniya Christine Lagarde
Shugabar hukumar Bada lamuni ta duniya Christine Lagarde (REUTERS)

Hukumar bada lamuni ta duniya IMF zata tura wata tawaga zuwa kasar Masar a makon gobe domin duba hanyoyin da zata bi wajen bada tallafin kudi ga kasar.Mai Magana da yawun hukumar ta IMF Gerry Rice yace zasu kai ziyara kasar ne don duba yadda za su iya taimaka wa kasar.

Talla

Tun bayan juyin juya halin da ya kifar da gwamnatin Hosni Mubarak, a shekarar bara, hukumomi a birnin Alkahira sun ki gayyatar hukumar ta IMF, don taimakawa a shawo kan matsalolin tattalin arzikin da suka dabaibaye kasar, da suka hada da gibin kasafin kudi.

Tun bayann juyin juya halin, tattalin kasar ya shiga halin tsaka mai wuya, sakamakon raguwar kudaden da ake samu ta hanyar yawon bude ido, do kuma komabayam da aka samu na masu zuba jari a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.