Kasashen duniya sun bukaci MDD daukar mataki akan Syria
Wallafawa ranar:
Kasashen Turai da Amurka da Kasashen Larabawa sun nemi kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kada kuri’ar la’antar zubar da jinin da ake yi a kasar Syria, inda Majalisar ta bayyana cewa sama da mutane 5,000 aka kashe a zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar Al Assad.
Talla
An bayyana cewa, kasashen Birtaniya da Faransa, da Jamus da Amurka ne zasu jagoranci matakin tunkarar Majalisar Dinkin Duniya.
Jakadiyar Amurka a kwamitin Sulhun, Susan Rice, ta bukaci sauran kasashen duniya domin bada goyan bayansu wajen haramta sayarwa Syria da makamai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu