Syria-Amurka-Birtaniya

Amurka da Birtaniya sun janye jekadunsu daga syria

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad sun yi da'ira a ofishin kedancin kasar Syria a Tunisia
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad sun yi da'ira a ofishin kedancin kasar Syria a Tunisia Reuters / Zoubeir Souissi

Kasar Amurka da Birtaniya sun janye jakadunsu daga kasar Syria saboda fargabar tsaro da rashin amincewa da yadda ake ci gaba da murkushe masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Bashar al Assad.

Talla

Birtaniya ta janye jakadanta amma Amurka ta rufe ofishin jekadancinta al’amarin da Obama ya bayyana cewa ya sha banban da rikicin kasar libya inda kasashen yammaci suka shiga tsakani wajen kawo karshen Kanal Gaddafi.

Sakataren harakokin wajen Birtaniya Williams Hague yace sun gayyaci Jakadan kasar ne na Birtania domin nuna rashin amincewar kasar game da yadda lamurra ke gudan a kasar Syria.

A cewar Williams Hague yanzu Birtaniya zata tura wasu sabbin matakan karya kasar Syria, tare da neman Majalisar Dinkin Duniya daukar matakan daya dace domin kawo karshen zubar da jini da ake samu a cikin kasar

Shugaban Amurka Barack Obama yace suna bin abubuwansu ne bisa tsarin diflomaciya.

Bayanai daga kasar ta Syria na nuna cewa a ajiya rayukan mutane akalla 48 aka rasa, sakamakon ruwan rokoki da jami’an tsaron Gwamnati suka yi ta aikewa akan Jama’a a birnin Homs.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI