Amurka

An bada kyautar Oscar ga fitattun masu shirya fina-finai na duniya

Jean Dujardin
Jean Dujardin AFP PHOTO Robyn BECK

Jean Dujardin ya lashe kyautar jarumin fina finan da ya fi kowa fice a shekarar da ta gabata, a wajen bikin karrama gwarzayen Oscar na bana.Dujardin Dan kasar Faransa, ya doke George Clooney da Brad Pitt, a fim dinsa na The Artist. 

Talla

Meryl Streep, ta lashe kyuatar mata, a rawar da ta taka a fim din The Iron Lady, wajen kwaikwayon Tsohuwar Fira Ministar Birtaniya, Margareth Thatcher.

Christopher Plummer, mai shekaru 82 na daga cikin wadanda suka lashe kyaututuka.

Plummer, mai shekaru 82, ya lashe kyautar Oscar da ake karrama wadanda sukayi fice a harkar fina finai, saboda rawar da ya taka a fim din Beginners.

Wasu daga cikin wadanda suak samu nasara, sun hada da Octavia Spencer, da ta lashe kyautar wadda tafi taimakawa jarumin shiri, a fim din The Help.

Sauran sun hada da Sandra Bullock, Asghar Farhadi, Kirk Baxter, da David Fincher.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI