Isa ga babban shafi
Amurka

Romney na Jam'iyyar Republican na kan gaba bisa zaben tantance gwani

Mitt Romney
Mitt Romney REUTERS/Brian Snyder
Zubin rubutu: Suleiman Babayo | Bashir Ibrahim Idris
Minti 1

Mitt Romney ya samu gagarumar nasara a zaben fidda gwanin Jam’iyar Republican da aka yi a Jihohi 10 na kasar Amurka, inda ya samu rinjaye a Jihohin Alaska, Idaho, Massachusetts, Vermont, Virginia da Ohio.Rick Santorum dake bi masa, ya lashe Jihohin North Dakota, Oklahoma da Tennessee, yayinda Newt Gingrich ya lashe Georgia. 

Talla

Bayan nasarar, Romney ya yiwa Shugaba Barack Obama na Jam'iiar Democrat mai mulki, shagube kan rashin aikin yi. Inda ya ce shugaban kasa da jami’ansa kullum suna shaida cewa, ana samun ci gaba, amma Amurkawa milyan 24 ba su da aiyukan yi, kuma samun kashi takwas na Amurkawan da basu da aikin yi, bai dace da Amurka ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.