Karamin Minsitan kasar Syria ya sauya sheka zuwa bangaren adawa
Wallafawa ranar:
Karamin ministan man fetur na kasar Syria Abdo Hussameddine, ya bayyana murabus daga kan mukamin, domin shiga cikin jerin masu adawa da gwamnatin shugaba Bashar Al-Assad, kamar yadda ya sanar ta Video da 'yan adawa suka yada ta shafin Youtube ta nunar.Gwamnatin kasar Amurka ta nemi majalisar dokokin kasar da cewa kar ta haifar da cikas wajen hanawa kasar Rsha shiga cikin hukumar kasuwanci ta duniya, sakamakon matsayin da Rashar ta dauka a rikicin kasar ta Syria.Wakilin Amurka mai kula da harakokin kasuwancin kasashen ketare Ron Kirk, ya koka a gaban 'yan majalisar dattawan Amurka, dake nazarin wata doka ta 1974 da kasashe Mambobin MDD 153 suka sakawa hannu, da ta haramtawa kasar Rasha shiga cikin hukumar kasuwancin, dokar dake yinkurin da Amurka ke yi na jawo kasar Rasha a hukumar.
Shugaban kwamitin jin kai na Majalisar Dinkin Duniya Valerie Amos, na kasar Syria yanzu haka a daidai wani lokaci da kungiyar agaji ta sami shiga da kayan agaji zuwa yankin Baba Amr inda aka rasa rayuka da dama.
Hukumomin kasar ta Syria sun bari kungiyar agajin ta Red Cresent sun kutsa kai yankin na Homs inda aka yi raga-raga da garin, bayan sun kwashe kwanaki biyar suna neman izinin shiga amma an hanasu.
Kakakin kungiyar Uwargida Carla Haddad ta fadi a Geneva cewa ayarin suna yankin Baba Amr yanzu haka.
Sai dai kuma Gwamnatin kasar Syria ta hana wasu kungiyoyin agajin biyu shiga yankin domin kwashe mutanen da suka jikkata, da kuma bada kayan agaji da ake matukar bukata a yankin.
Duk wannan dan bari da akay i wasu masu agajin su shiga na biyo bayan ziyarar da Shugaban kwamitin jinkai na MDD Valerie Amos wadda ta gana da Ministan waje na Syria Walid Muallem, wanda yayi alkawarin baiwa ayarin cikakken hadin kai.
Shima dai jakadan musamman na MDD da kungiyar kasashen Larabawa Kofi Annan na kan hanyarsa zuwa Syria akokarin kawo karshe rikicin kasar
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu