Isa ga babban shafi
Iran-Syria

Iran ta goyi bayan Syria tare da zargin Amurka

Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad sun yi da'ira a kasar Syria
Wasu masu zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad sun yi da'ira a kasar Syria REUTERS/Handout
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
1 Minti

Gwamnatin kasar Iran ta nuna goyon bayanta ga kasar Syria tare da zargin kasar Amurka da kasashen Larabawa wajen haddasa rikicin da ya tarwatsa kasar, A cewar Ministan harakokin wajen Iran, Hossein Amir Abdollahian, Gwamnatin Iran tana bayan gwamnatin Syria da al’ummarta.

Talla

A cewar Ministan kasashen Turai ne da kasashen Larabawa suka hura wutar rikicin Syria, sai dai yace gwamnatin Iran zata goyi bayan sasanta rikicin kasar ta hanyar Siyasa.

Gwamnatin Iran ta musanta zargin da Amurka ke mata na taimakawa gwamnatin Syria da makamai domin karya masu zanga-zanga.

A ranar Lahadi ne Kofi Annan manzo na musamman da Majalisar Dinkin Duniya ta aika a Syria ya fice kasar ba tare da sasanta rikicin da aka bayyana daruruwan mutane suka mutu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.