Amurka

Romney ya lashe zaben Fitar da gwani a wasu Jahohin Amurka uku

Mitt Romney, Dan takarar neman kujerar Shugaban kasa karkashin Jam'iyyar Republican a kasar Amurka
Mitt Romney, Dan takarar neman kujerar Shugaban kasa karkashin Jam'iyyar Republican a kasar Amurka REUTERS/Darren Hauck

Mitt Romney ya lashe zaben fitar da gwanin masu takarar neman kujerar Shugaban kasar Amurka karkashin Jam’iyyar Republican a Jahohin Winsconsin da Maryland da Washington DC. Akwai tazara yanzu tsakanin Romney da sauran abokan takarar shi.

Talla

Mitt Romney yanzu ya sha gaban abokin takararsa Rick Sontorum. Hakan kuma ke nuna alamun Romney ne zai kara da Obama a zaben shugaban kasa.

Mista Romney ya bayyana farin ciknsa da wannan nasarar da ya ke samu, kuma kamar kullum yakan yi amfani da wannan damar domin kai hari ga manufofin Shugaba Barack Obama na Jam’iyar Democrat.

Romney yanzu ya samu nasara a Jahohi 24, inda babban abokin karawar shi Santorum ya samu nasara a jahohi 11.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.